Isra′ila ta kai hari Gaza | Labarai | DW | 18.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta kai hari Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare kan yankin zirin Gaza, bayan raunin da wasu sojojin kasar suka ji sakamakon tashin bom jiya Asabar a yankin Falasdinawa.

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare kan yankin zirin Gaza, bayan raunin da wasu sojojin kasar suka ji sakamakon tashin bom a ranar Asabar a yankin Falasdinawa. Ma'aikatar tsaron Isra'ilar ta ce ta afka wa akalla sansanonin shida da ke yankin na Falasdinawa, saboda amannar da suka cewar falasdinawan sun dasa boma-boman da gangan a Juma'ar da ta gabata, kuma suka ajiye tutarsu.

Kamfanin dillancin labaran Falsdinu Wafa, ya ce wasu makamai masu linzami da Isra'aila ta harba, sun lalata gidaje a wurare uku a Gaza. Lamura dai sun kara tabarbarewa tsakanin Isra'ila da Falasdinu ne tun cikin watan Disamba, lokacin da Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana amincewa da birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.