Isra′ila ta kai hare-hare kan Siriya | Labarai | DW | 09.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta kai hare-hare kan Siriya

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare ta sama a Siriya a wuraran da sojojin gwamnatin ke harba ma ta makamai masu linzami a wani maratanin daukar fansa.

Kamfanin dilancin labarai na Siriya SANA, wanda ya ce Isra'ilan ta fara kai hare-haren ne, daga tuddan Golan. Ya ce hare-haren sun lalata wasu na'urori na wani sansanin soji tare da kashe soji daya kana wasu biyar suka jikkata.Tun lokacin da aka fara yakin Siriyar a shekara ta 2011 Isra'ilan ta  kai hare-hare sama da guda dari a Siriyar a sansannin sojoji na gwamnatin da kuma na dakarun Hizbollah na Iran da ke taimaka wa gwamatin Bashar Al Assad.