1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta binne gawar karshe da aka dawar daga Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
January 28, 2026

A wannan Larabar ce (28.01.2026) Isra'ila ta yi jana'izar mutum na karshe da aka yi garkuwa da shi daga harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba 2023.

https://p.dw.com/p/57dvL
Hoto: Ilia Yefimovich/AFP/Getty Images

 A wurin jana'izar Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewar, makiyan Isra'ila za su fuskanci mummunan hukunci idan sake irin hakan nan gaba.

Barazanar Netanyahu na zuwa ne yayin da Hamas ta shaida wa AFP cewa, ta shirya tsaf don mika cikakken ikon Gaza ga kwamitin Falasdinu mai mambobi 15, da aka kafa a karkashin shirin tsagaita wuta da Amurka ke goyon baya.

Daruruwan mutane ne dai suka hallara a filin wasa na kudancin Isra'ila don jana'izar Ran Gvili, wanda ke zama mutum na karshe da aka dawar da gawarsa daga Gaza, wanda binne shi ya rufe shafin mummunan yanayin da kasar ta fada sakamakon harin Hamas a 2023.