Isra'ila: Dokar mallakar fili a Gabar Yamma da kogin Jordan
February 16, 2026
Gwamnatin Isra'ila ta amince sabuwar dokar mallakar fili a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Kazalika duk wanda ya yi ikrarin mallakar filin a yankin zai nuna takardar shaidar mallaka, sai dai ana ganin hakan zai yi wuya sakamakon yawancin filayen da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan ba a yi musu rajista a hukumance ba.
Karin bayani: Isra'ila za ta samar da sabbin matsugunnai a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Sai dai kuma hukumomin Falasdinu sun yi watsi da wannan shirin, inda suka yi ikrarin cewa, Isra'ila na kokarin mamaye yankin ne. Kazalika Kungiyar Tarayyar Turai da kuma wasu kasashen Larabawa sun caccaki matakin.
Sai dai ministan tsaron Isra'ilar, Israel Katz ya ce hakan na da matukar mahimmanci saboda tsaro da kuma iko ga Isra'ilar a yankin. Fiye da Yahudawa 'yan kama wuri zauna 700,000 ne ke zaune a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus tare da Falasdinawa kimanin miliyan uku.