Isra′ila sabuwar babbar kawar Afirka? | Siyasa | DW | 13.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Isra'ila sabuwar babbar kawar Afirka?

Tsawon shekaru Afirka na zaman babbar kawar Palasdinu. Amma yanzu kasashen Afirka da dama na inganta hulda da Isra'ila. Sai dai sabon hadin kan na da nakasu.

A shekarar da ta gabata ta 2016 Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya kai ziyara mai cike da tarihi zuwa nahiyar Afirka, inda ya zama shugaban gwamnati Isra'ila na farko da ya kai irin wannan ziyara cikin shekaru da dama da suka gabata. Kasashen na Afirka na kara karfafa danganta da Isra'ila, duk da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Shi dai Firaminista Benjamin Netanyahu ya kai ziyara zuwa kasashen Kenya, da Yuganda, da Habasha gami da Ruwanda, inda ya samu tarba ta kasaita. Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya nuna muhimmancin aiki da Isra'ila a fannonin samar da ci-gaba. A ziyara ta biyu Firaminista Netanyahu ya yi jawabi a gaban shugabannin kasashen yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO.

Im Juni hielt Netanjahu auf dem Gipfel der westafrikanischen Staatengemeinschaft ECOWAS eine Rede

A watan Yuni Netanyahu ya yi jawabi a gaban taron kolin kungiyar ECOWAS

Wani abu da ake ganin ya fara janyo samun kusanta tsakanin Afirka da Isra'ila shi ne lokacin da Afirka ke gwagwarmayar kawo karshen mulki mallaka kamar yadda Steven Gruzd na wata cibiyar kula da harkokin kasashen ketare da ke Afirka ta Kudu ke cewa:

"An kafa kasar Isra'ila a shekarar 1948 sannan a shekarun 1950 da shekarun 1960 take da dangantaka mai karfi da Afirka. Akwai ma'aikatan ayyukan ci-gaba na Isra'ila da dama da suke aiki, kana akwai 'yan Afirka da suke karatu a Isra'ila, da ofisoshin jakadanci fiye da 30. Akwai tunanin nuna rashin yarda da mulkin mallaka, Isra'ila ta kawar da 'yan mulkin mallaka na Birtaniya kuma lokacin Afirka tana haka, shi ya sa aka samu dangantaka mai karfi."

Amma lamarin ya sauya bayan yakin kwanaki shida na shekarar 1967 tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa, inda ta mamaye wasu yankunan kasashe. Cikin wuraren da Isra'ila ta mamaye akwai yankin Sinai na kasar Masar, inda kasar ta Masar ta zargi Isra'ila da mamaya a nahiyar Afirka. Haka ya janyo kasashen Larabawa sun shawo kan Afirka bisa katse hulda da Isra'ila. A cikin fiye da kasashe 30, hudu kacal suna rage masu dangantaka da Isra'ila. Wannan ya shafi danganta a kungiyar Tarayyar Afirka inda aka amince da Palasdinawa a matsayin 'yan kallo, amma Isra'ila ba ta samu damar ba.

Karancin masu adawa da Isra'ila a Afirka

Yanzu lamura sun sauya. Tun bayan kawar da Shugaba Mu'ammar Gaddafi na Libiya aka kawo karshen babban mai adawa da Isra'ila a kungiyar Tarayyar Afirka. Lokacin da Shugaba Donald Trump na Amirka ya kira Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila babu wata gagarumar zanga-zanga daga nahiyar Afirka. Ga abin da Martin Oloo masanin harkokin siyasa a Kenya ke gani:

"Isra'ila kowane lokaci tana shirye ta bayar da taimako kan aikin soja, game da horo da sauran abubuwa. Galibin kwararrun sojojin da suke tsaron manyan jami'an gwamnati sun samu horo daga Isra'ila. Domin haka akwai taimako na soja, da tsaro da Afirka ke ci gaba da samu daga Isra'ila."

Hadin kan aikin soja da raya kasa

Israelische Experten sollen kenianische Sicherheitskräfte bei der Abwehr des Terroranschlags auf das Westgate-Einkaufszentrum beraten haben

Jami'an tsaron Isra'ila sun ba da shawara ga dakarun tsaron Kenya don murkushe harin da aka kai kan kantin Westgate

Burin samar da lantarki ga mutane miliyan 600 nan da shekara ta 2030 a Afirka gami da fasaha daga Isra'ila sun taimaka ga wannan hulda. Steven Gruzd na cibiyar bincike kan harkokin kasashen ketare da ke Afirka ta Kudu ga abin da yake gani:

"Ina tsammni 'yan siyasa na Afirka sun kasance masu nuna sanin ya kamata, ba sa bai wa akida fifiko kamar abin da yake faruwa a baya. Goyon baya ga Palasdinawa babu karfi kamar yadda abin yake a wani lokaci da ya gabata."

Har yanzu akwai sauran aiki, domin Firaminista Netanyahu ya bukaci Isra'ila ta zama 'yar saka ido a kungiyar Tarayyar Afirka kana wasu kasashen Afirka da Musulmai ke da rinjaye kan nuna dari-dari da Isra'ila musamman kan rikicin kasar da Palasdinu.

Sauti da bidiyo akan labarin