Isra′ila na shirin yin kuskure | Labarai | DW | 24.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila na shirin yin kuskure

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce Isra'ila za ta tafka kuskure da zai sanya ta yi da na sani in har ta dauki matakin kai hari a kan Iran.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry Iran

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry Iran

Kerry ya bayyana haka ne a wani shiri mai taken "Today" da tashar talabijin ta NBC ke yadawa, inda ya ce duk wani hari da Isra'ilan za ta kai na soja ko kuma na kafar Internet da ake kira da Cyber Attack kuskure ne za ta tafka gagarumi wanda kuma zai haifar mata da yin da na sani mara amfani. Ya kara da cewa illar kuskuren ba wai a kan Isra'ilan kawai za ta tsaya ba har ma da yankin Gabas ta Tsakiya baki daya. Tun dai bayan da aka cimma yarjejeniya kan batun makamashin nukiliyar Iran din tsakanin Iran da manyan kasashe shida masu fada aji a duniya, Isra'ila ke ci gaba da yin kumfar baka da kuma nuna adawarta da matsayar da aka cimma din inda ta sha alwashin daukar matakin da take ganin ya dace a kan Iran din ba tare da yin shawara da kowa ba.