1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Hamas sun gaza cimma matsaya kan yakin Gaza

May 5, 2024

Jagoran Hamas, Ismail Haniyeh ya zargi Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da yin zagon kasa ga kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Alkahiran Masar.

https://p.dw.com/p/4fWUK
Jagoran kungiyar Hamas, Ismail Haniyey
Jagoran kungiyar Hamas, Ismail HaniyeyHoto: Vahid Salemi/AP Photo/picture alliance

Jagoran Hamas, Ismail Haniyeh ya ce Netanyahu na kirkiro dalilai na babu gaira babu dalili wadanda za su kara fadada yakin Gaza da aka kwashe tsawon watanni bakwai ana yi. Shi ma a faifan bidiyon da ya wallafa a wannan Lahadin, Netanyahu ya zargi Hamas da jan kafa wajen amince dadaftarin bukatar dakatar da yakin, ya na mai ikrarin Isra'ila za ta ci gaba da yaki har sai ta ga abun da ture wa buzu nadi.

karin bayani: Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhu

A yanzu haka dai babu wani karfin gwiwa kan iya cimma yarjejeniyar a wannan Lahadin yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da nuna wa juna dan ratsa.