IS ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin Berlin | Duka rahotanni | DW | 20.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

IS ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin Berlin

Kungiyar IS mai da’awar jihadi ta ayyana daukar alhakin mummunan harin da aka kai kasuwar Kirsimeti a Berlin yayin da Jami’ai suka yi kashedin cewa  mai yiwuwa wanda ya kai harin ya shiga buya.

Kungiyar masu da’awar Jihadi IS a ranar Talatar nan ta yi ikirarin cewa ita ce ke da alhakin harin da aka kai kasuwar Kirsimeti a Berlin a cewar kafar yada labaran kungiyar Amaq.

Tun da farko masu gabatar da kara na Jamus sun sanar da sakin wani dan kasar Pakistan mai shekaru 23 da haihuwa wanda aka tsare dangane da harin wanda aka kai da wata babbar mota, saboda rashin kwakkwarar hujja.

Deutschland PK Thomas De Maziere über Anschlag in Berlin (Getty Images/AFP/J. McDougall)

Ministan cikin gida Thomas de Maiziere

Bayan sanarwar sakin wanda ake zargin, Ministan cikin gida Thomas de Maiziere ya shaida wa gidan talabijin na ZDF cewa hakika ba za a iya kau da tsammanin cewa maharin ya shiga buya ba. Ya kuma yi gargadin cewa ba zai yi hanzarin yanke hukunci ta fuskar siyasa a kan lamarin ba.

A ranar Litinin hukumomi suka kama mutumin wanda ke neman mafaka da zargin tuka motar da ta afka kann cincirindon jama’a a kasuwar Kirsimeti a tsakiyar Berlin wanda ya hallaka mutane 12 tare da jikkata wasu jama’ar da dama.

Tun ma dai kafin de Maiziere ya bada wannan sanarwa rundunar 'yan sandan Berlin ta amince cewa mai yiwuwa mutumin da ta kama ba shi ne wanda ya kai harin ba. A saboda haka ta gargadi jama’a su kasance cikin takatsantsan.