IS na ci gaba da kashe mutane a Iraqi | Labarai | DW | 03.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS na ci gaba da kashe mutane a Iraqi

A ci gaba da ayyukan ta'addanci da kai hare-hare da 'yan kungiyar IS ke yi a Iraqi, sun hallaka wasu 'yan Yazidi 25 a Iraqi.

Ta'addancin kungiyar IS

Ta'addancin kungiyar IS

Wani dan majalisar dokokin kasar Iraqi mai suna Mahma Khalil ya sanar da hakan inda ya ce, baki dayan mutanen ta suka kasance 'yan Yazidi an hallaka su ne a sansanin da IS din ke tsare da su bayan ta kama su wanda ke garin Tal Afar na Iraqin. Khalil ya kuma jaddada cewa yana da yakinin akwai 'yan Yazidin masu tarin yawa a hannun kungiyar ta IS har kawo yanzu. Kungiyar ta IS dai da ke danganta kanta da Musulmi mabiya Sunna na daukar 'yan Yazidi da kuma Musulmi mabiya Shi'a a matsayin kafirai da suka can-canci hukuncin kisa.