IS: Libiya ta neman tallafin Larabawa | Labarai | DW | 16.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS: Libiya ta neman tallafin Larabawa

Gwamnatin Libiya ta bukaci kasashen Larabawa da su kai jerin hare-hare a kan mayaƙan ƙungiyar nan ta IS da ke gwagwarmaya da makamai a birnin Sirte.

Wannan kira da gwamnatin Libiya din ta yi na zuwa ne daidai lokacin da mayakan na IS da ke ci gaba da tada kayar baya a yankin.To sai dai ya zuwa yanzu ƙasashen na Larabawa ba su kai ga cewa komai game da wannan kira ba, kuma babu tabbaci da ake da shi ko za su amince da wannan buƙata ta Libiyan ko akasin haka.

'Yan ƙungiyar ta IS dai na amfani da ƙalubalen tsaron da Libiya ɗin ke fuskanta wajen cigaba da kankane wasu yankuna a fufutukar da suke yi ta faɗaɗa daular da su ke son girkawa.