1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta Kalubalanci Amirka

August 27, 2018

Masana shari'a a Iran za su bukaci kotun duniya ta tilasta wa Amirka janye takunkuman da ta dora wa kasar.

https://p.dw.com/p/33oqA
Den Haag Internationaler Gerichtshof ICJ Entscheidung Bolivien Chile
Hoto: Getty Images/AFP/J. Lampen

Lauyoyi a Iran sun shirya gabatar da bukatar kotun duniya ta tilasta wa gwamnatin Amirka janye takunkuman da ta kakaba wa kasar, saboda saba doka da hakan ya yi.

Bukatar lauyoyin ta yi nunin cewa matakin na Amirka wanda ya fara nakasa arzikin kasar ta Iran, ya ci karo da yarjejeniyar hulda tsakanin kasashen biyu da aka kulla a shekarar 1955.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ta Amirka, wacce za ta amsa tambayoyin a gobe Talata, ba ta kai ga cewa komai ba.

Sai dai ana sa ran lauyoyin Amirka a na su bangaren, na iya musanta cewa kotun ba ta hurumi kan wannan batu, hasali ma a ganinsu, wannan yarjejeniya ce da babu ita.

Kotun ta duniya dai, kotu ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke sasanta takamma tsakanin kasashe.