Iran ta yi kira ga hadin kan Musulmi | Labarai | DW | 24.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi kira ga hadin kan Musulmi

Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa tsiraru 'yan Shi'a a Afghanistan, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80 tare da jikkata wasu 231 a ranar Asabar.

Da ya ke magana ta shafinsa na Twitter, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammand Javad Zarif, ya yi kira ga hadin kan Musulmi na mazahabar Shi'a da kuma ta Sunna, domin yakar masu tsatsauran ra'ayi, inda ya ce wannan hari na a matsayin wani sabon salo na ta'addanci da kungiyar ta IS ke aikatawa.

Daga nashi bangare mai magana da yawun ma'aikatar diflomasiyyar kasar ta Iran Bahram Ghassemi ya ce idan har babu hadin kai tsakanin kasahe, to akwai wahala a kawo karshen iri-irin wadan nan masu tada zaune tsaye a duniya. Kasar ta Iran dai wadda akasarin al'ummarta ke bin mazahabar Shi'a, na da doguwar iyaka da kasar ta Afghanistan.