Iran ta sake yi wa Amirka barazana | Labarai | DW | 02.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta sake yi wa Amirka barazana

Hukumomi a Iran sun ce a shirye kasar take domin mayar da martani a kan duk wani nau'i na karfin soja da Amirka za ta iya yi ke yi wa kasar, ko da da me Amirkar ke gadara.

Babban kwamandan mayakan juyin juya hali na kasar Iran Janar Hossein Salami, ya ce shirye kasar take domin mayar da martani a kan karfin soja da Amirka ke yi wa kasar, duk da zafafa kalamai da Shugaba Trump wanda wa'adinsa ke zuwa karshe yake yi.

Janar Hossein Salami, na magana ne a wani biki da aka yi a jami'ar birnin Tehran, bikin da aka yi domin tunawa da kisan kwamadan yakin kasar, Janar Qassem Soleimani, da Amirka ta yi a farkon watan Janairun bara a Iraki.

A lokacin ma dai Iran din ta kai harin ramuwar gayya da makamin mai linzami a sansanin sojan Amirka da ke Irakin, inda akalla wasu sojojin Amirkar 100 suka sami matsala ta kwakwalwa da sauran munanan raunuka.

A cikin kalamansa a lokacin taron na jami'ar Tehran, kwamandan mayakan na Iran, Janar Hossein Salami, ya ce Iran ba ta da wata matsala ko taraddadin iya mayar wa da Amirka kowane irin martani.