1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran ta kore yiwuwar kashe Shugaba Raisi aka yi

May 25, 2024

Hukumomi a Iran sun ce ba lallai ba ne hadarin da marigayin shugaban kasar ya yi, ya zamo mai alaka da wata kutungwila ko makarkashiya daga wani yanki na duniya.

https://p.dw.com/p/4gH8K
Hoto: Azin Haghighi/MOJ News/Zuma/IMAGO

Hafsan hasoshin dakarun gwamnatin kasar Iran, ya ce ga dukkan alamu mutuwar shugaban kasar Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen kasar gami da wasu jami'ai shida a karshen makon jiya, hadari ne kawai da ya zo.

Wannan labarin ya fito ne daga rahoton farko a kan bincike da aka gudanar kan hadarin, da jagorancin sojojin Iran din ya wallafa.

Shi dai jirgin sama mai saukar angulun da ke dauke da marigayi Shugaba Raisi da manyan jami'an, ya kama da wuta ne a lokacin da ya fadi a ranar Lahadi yayin da ya hadu da kasa.

Masu bincike sun ce babu alamar hujin harbi ko wani abu da ya kama da hakan a jinkin tarkacen jirgin, abin da ke iya kore duk wasu shakku kan harbe jirgin aka yi.

Amma kuma wani hoto da wani ya wallafa a shafin X da ake kira Twitter a baya, ya nuna cewa kakkabo jirgin aka yi da makami mai amfani da haske daga sama.

Sai dai wani bincike da tawagar bin diddigi na DW, ya ce babu gaskiya cikin ikirarin da mai hoton ya yi.