1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta cigaba da shirin nukiliya

Abdul-raheem Hassan
November 1, 2021

Bayan da kasashen Amirka da Birtaniya da Faransa da ma Jamus suka nuna damuwa kan shirin nukiliyar Iran a taron G20, Tehran ta sake cewa shirin nata na zaman lafiya ne.

https://p.dw.com/p/42R1J
Iran Atomanlage Nuklear Energie
Hoto: AFP/Getty Images

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ya shaida wa manema labarai a birnin Tehran cewa, matsayin kasashen yamma ba su dace da hakikanin gaskiya ba, kuma ba za su haifar da sakamako mai ma'ana ba.

Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya shida na samar da mafita mai dorewa kan rikicin shirin nukiliyarta na ci gaba da tabarbarewa ne tun bayan da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya yi watsi da yarjejeniyar a watan Mayun 2018 tare da kakaba wa Iran takunkumai.