Iran na shirye wajen tattauna shirin nukiliyarta | Labarai | DW | 25.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran na shirye wajen tattauna shirin nukiliyarta

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya tabbatar da cewar, makaman nukiliya da na kare dangi basu da gurbi a tsarin tsaron kasarsa.

Sabon Shugaban na Iran ya fada wa babban zauren Majalisar Dunkin Duniya cewar, a shirye Tehran take ta shiga tattaunawa a kan shirin nukiliyarta mai sarkakiya. Da ya ke jawabi a taron na shekara shekara a birnin New york din Amurka, Rouhani sake jaddada cewar shirin inganta sinadran Atom na kasarsa bashi da wata barazana ga duniya kamar yadda ake zargi, kasancewar makaman nukiliya basa cikin tsarin matakan tsaron Iran.

" Nukiliya da sauran makaman kare dangi basu da gurbi a tsarin tsaron Iran. Manufar kasarmu ita ce mu kawar da duk wani tsoro ko kuma wata damuwa da ake dashi, a kan shirin nukiliyar Iran na samar da zaman lafiya" .

Sakamakon zargin da ake wa Iran na fakewa da shirin inganta samar da wutar lantarki wajen kera makaman Nukiliya, ya jagoranci kasashen yammaci kakaba wa kasar jerin takunkumi, wanda sabon shugaba Rouhani ya ce basa bisa ka'ida. Tun bayan hawansa karagar mulki a watanni hudu da suka gabata dai Rouhani ya dauki matakan inganta dangantakar diplomasiyya da kasasahen yammaci

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu