1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Mutane 170 sun mutu a hadarin jirgin sama

Gazali Abdou Tasawa
January 8, 2020

Rahotanni daga kasar Iran na cewa mutanne akalla 170 suka halaka a cikin wani hadarin jirgin saman fasinja na kamfanin Ukraine International Airlines da ya wakana a wannan Laraba.

https://p.dw.com/p/3VsET
Iran Flugzeugabsturz
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Noroozi

Jirgin saman samfurin Boeing 737 dauke da mutane 176 da suka hada da fasinjoji 167 da ma'aikatan jirgin guda tara ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga filin jiragen sama na birnin Teheran zuwa birnin Kiev.

Kafofin yada labaran kasar ta Iran sun bayyana cewa bayanan farko da aka samu na cewa jirgin ya fado ne kusa da birnin Chahriar da ke a yammacin birnin na Teheran inda nan take ya kama da wuta.

Shugaban kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross reshen kasar ta Iran ya ce da wuya a iya samun wanda ya fita da rai a cikin hadarin jirgin wanda ya zuwa yanzu ba a danganta shi ba da rikicin da ke wakana a yankin na golf ba.