1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Iran a Iraki ya haifar da fargaba

Zulaiha Abubakar
January 8, 2020

Kamfanonin jiragen saman wasu kasashe sun dakatar da jigilar matafiya zuwa kasashen Iraki da Iran, biyo bayan harin ramuwar gayya da kasar Iran ta kai kan sansanin sojojin Amirka da ke Iraki.

https://p.dw.com/p/3Vtf6
Lufthansa-Flugzeug und Aufschrift mit Werbung für klimafreundliches Fliegen
Hoto: DW/A. Spaeth

Kamfanin jiragen sama na Lufthansa mallakar kasar Jamus da gungun jiragen Hadaddiyar Daular Larabawa, sun bi sahun kasashen da suka haramtawa jiragensu ratsawa ta kasashen Iran da Iraki saboda fargabar tsaro. Wannan dai ba shi ne karo na farko da jiragen sama suke gaggawar daukar matakan tsaron lafiya da dukiyoyin fasinjoji a lokutan rashin tabbas ba. A shekara ta 2014 ma jirage sun dauki irin wannan matakin gaggawar biyo bayan faduwar wani jirgin Malesiya mai dauke da fasinjoji 298.