1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Iran da hukumar IAEA

Mahmud Yaya Azare LMJ
August 27, 2020

Iran ta amince da bai wa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya IAEA, damar binciken wasu cibiyoyi biyu da ake zargin tana bunkasa makamashin nukiliya cikinsu a asirce.

https://p.dw.com/p/3hahV
Iran Atomenergie | Verhandlungen IAEA | Rafael Grossi & Hassan Rohani, Präsident
Shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi da shugaban kasar Iran Hassan RohaniHoto: Reuters/Official Presidential Website

Iran din ce dai da kanta ta gayyaci jami'an hukumar ta IAEA, wadanda  suka yi ganawar kwanaki biyu da mahukunta a birnin Tehran, kafin su cimma wannan matsaya. Shugaban Hukumar Kula da Makashin Nukiliya na kasar ta Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya yi karin haske: "Mun cimma matsaya cewa hukumar ta IAEA za ta gudanar da binciki abin da take tababa a kansa ne kawai a wadanan cibiyoyin biyu. Ta kuma amince ba za ta gabatar bincika abubuwan da ba ta da tababa a kansu ba. Babu wani abun da muke boyewa, amma 'yancin kasarmu zai sa mu ringa taka-tsan-tsan."

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya zargi Isra'ila da bai wa hukumar ta IAEA bayanan sirri na karya domin yi wa kasarsa batanci da hanata bunkasa makamashin nukiliyarta da take amfani da shi kan bukatun fararen hula.

Iran PK Außenminister Mohammad Javad Zarif
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif Hoto: picture-alliance/AA/Y. Keles

To sai dai shugaban Hukumar kula da Makashin Nukiliyar ta Duniya Rafael Grossi ya nunar da cewa, binciken nasa ba shi da alaka da yarfen da kasashen na Iran da Isra'ila ke yi wa juna: "Wannan aiki ne na tsawon lokaci da muka jima muna yi a kasar, ba tare da yin la'akari da cece-kucen siyasar da ake ba. Muna gudanar da aikin ba tare da yin wata rufa-rufa ko nuna son kai ba, kuma haka zamu ci gaba da yi a yanzu dama nan gaba."

 Amirka dai a ta bakin ministan harkokin wajenta Mike Pompeo ta siffanta wannan matsayar da aka cimma da tsantsar yaudara da ta ce za tai kokarin yi mata zagon kasa. A yayin da Rasha wacce ta bayyana farin cikinta matuka dangane da cimma matsayar ke cewa, hakan babban ci gaba ne da ke  tabbatar da cewa za a iya warware matsaloli da dama ta hanyar tatatunawa ne kadai, ba ta hanyar yin barazana ko gwada kwanji ba.