Iran ba zata yi watsi da shirinta na nukiliya ba, inji Ayatollah Khameni | Labarai | DW | 13.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ba zata yi watsi da shirinta na nukiliya ba, inji Ayatollah Khameni

Limamin Limaman ƙasar Iran Ayatollah Ali Khameini ya ce Iran ba zata yi ƙasa a guiwa ba a rikicin da ake yi da ita game da shirinta na nukiliya. Amirka ba zata yi nasarar kaskantar da Iran ba, inji Ayatollah Khameni a lokacin ganawarsa da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa a birnin Teheran, Mohamed El-Baradei. Kamar shugaban ƙasa Mahmud Ahmedi-Nejad shi ma Khameni ya jaddada cewa ƙasarsa ba zata taba yin watsi da shirin nukiliyar ba. Ya ce shirin don amfanin farar hula ne ta hanyoyin lumana. Amirka da sauran ƙasashen yamma na zargin Iran da hanƙoron mallakar makaman nukiliya a boye.