1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sandan Najeriya za su tunkari bata-garin yankin Igbo

May 18, 2021

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta kaddamar da sabon shirin kakkabe masu aikata laifuka a jihohin kabilar Igbo da ke Kudu maso Gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3tZjT
Nigeria I Überfall auf Gefängnis
Hoto: David Dosunmu/AP/picture alliance

Shirin da aka kaddamar a wanann Talata mai lakabin ''Operation Restore Peace'' na da zummar tunkarar masu aikata laifi a yankin ne ba ji ba gani kamar yadda wata sanarwa daga rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana. 

A watannin baya-bayan nan dai lamuran tsaro a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriyar sun dagule. A watan Afrilun da ya gabata, wasu bata-gari sun fasa wani gidan kaso a birnin Owerri na jihar Imo inda fursunoni sama da 1,800 suka arce daga hannun hukumomi.

 Ana dai zargin kungiyar nan mai rajin kafa kasar Biafra, wato, IPOB, da galibin wadannan laifuka. To amma kungiyar ta sha nanata cewa ta na kokari ne na ganin ta samar wa jama'ar yankin kyakkyawar makoma ta hanyar ballewa daga Najeriya wace suke ganin ta kasa biya musu bukata.