1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar matakin gaggawa kan yanayi

August 9, 2021

Shugabannin kasashen duniya, ka iya gaza cimma bukatar kawo karshen sauyin yanayi, in har ba su dauki matakan gaggawa kan kawo karshen gurbataccen hayakin da masana'antu ke fitarwa ba.

https://p.dw.com/p/3ylZr
Deutschland Braunkohlekraftwerk Niederaußem bei Bergheim
Hayakin na masana'antu ke fitarwa, na mummunan tasiri ga muhalli da yanayiHoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Kwamitin kwararrun masana kimiyya kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna gurbatar yanayin duniya ya kai matakin koli kan yaki da sauyin yanayi. Kwamitin ya ce ya zama tilas nan da shekaru 15, a aiwatar da matakin rage dumamar yanayin da zai tsayar da dumamar da duniya ke yi zuwa kasa da maki 1.5 a ma'aunin zafi. Cikin wani rahoton wanda wakilan kasashe 195 suka amince da shi, karkashin kwamitin kwararrun masana kimiyya kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira IPCC, ya yi nazari kan yanayin da kasashe masu arziki da marasa galihu suka samu kansu, sakamkon sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.

Karin Bayani: Muhawara kan ibtila'in ambaliyan ruwa

A shekara ta 2014 aka fitar da rahoton karshe, kuma masana kimiyya yanzu na cewa sauyin yanayi na da tasiri kan gobarar daji da ambaliyar ruwa gami da guguwa mai haddasa bala'i da ake samu, yayin da wasu kasashen ke fuskantar fari. Sonia Seneviratne ta cibiyar kula da yanayi da ke birnin Zurich na kasar Switzerland, ta ce rahoton ya nuna irin kasadar da duniya ke ciki idan ba a dauki mataki kan sauyin yanayin ba. A shekara ta 2015, shugbannin kasashen duniya sun yi alkawarin daukar matakin ganin dumamar duniya bai kai maki biyu a ma'aunin zafi ba nan da karshen karni, wanda haka ne zai hana jefa duniya cikin bala'i. 

Klimakonferenz Cop21 2015 in Paris
Har yanzu ba ta sauya zani ba, shekaru shida da taron muhalli na ParisHoto: picture-alliance/AA/A. Bouissou

Amma maimakon haka manufofin gwamnatoci na nuna yuwuwar samun dumamar duniyar da maki uku a ma'aunin zafi. A ganin Malte Meinshausen na cibiyar nazarin yanayi a Potsdam da ke Jamus, lokaci na kurewa. A sassan duniya ana kara samun ruwan sama da ke karuwa da kaso bakwai cikin 100 kan yadda aka saba, ga karuwar iska mai dauke da ruwan sama da ke haddasa bala'o'i a kasashe kana duniya na kara dumama.

Karin Bayani: Trump: Amirka ta fita yarjejeniyar Paris

Ana ganin nan zuwa shekara ta 2050, dalar kankara da ke arewacin duniya za ta narke. Veronika Eyring da ke cibiyar kula da sararin samaniya ta Jamus ta ce, abin da ake fada ne duniya ke ganinsa a zahiri. Manyan abubuwa da suke haifar da sauyin yanayi sun hada da makamashin kwal da man fetur gami da iskar gas. Ga Doulas Maraun na cibiyar kula da sauyin yanayi ta duniya komai kankantar mataki idan aka dauka yana da tasiri. Ana sa ran shugabannin kasashen duniya za su tattauna rahoton, domin samar da mafita.