1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta tura kumbo zuwa duniyar rana

Binta Aliyu Zurmi
September 2, 2023

Hukumar binciken sararin samaniyar kasar Indiya ta tura kumbo zuwa duniyar rana domin zurfafa bincike a kan ta da ma sauran abubuwan da suka zagayeta.

https://p.dw.com/p/4VsLx
Indien Aditya L1
Hoto: AP

Kumbon da aka yi wa lakabi da Aditya-L1 wanda ke nufin rana da Indiyanci an harba shi ne a yau Asabar.

Wannan sabon shirin na zuwa ne mako guda bayan nasarar da Indiya ta yi na zama kasa ta farko da je kusa da duniyarwata da 'yar tazara.

Shirin tura kumbo zuwa rana na da zummar yin bincike a kan iskar da ke zagaye da rana da ma sauran halittu gami da yadda ake samu haske a duniyarmu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gudanar da bincike a duniyar rana ba, a baya hukumar NASA ta kasar Amirka da hukumar nazarin sararin samnaiyar Turai sun yi nasu, sai dai wannan na Indiyar yana da banbanci da wadancan.