Indiya: Mutane 27 sun mutu a zanga-zanga | Labarai | DW | 26.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indiya: Mutane 27 sun mutu a zanga-zanga

Rahotanni daga kasar Indiya na nuni da cewar adadin wadanda suka mutu a rikicin kasar ya haura zuwa mutane 27, yayin da sama da wasu 200 suka jikkata.

Firaministan Indiyan, Narendra Modi ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankula a kan boren da ke ci gaba da daukar sabon salo. Wannan dai shi ne bore mafi muni da birnin na New Delhi ke fuskanta, a dangane da haka ne ma Mr Modi ya bukaci sojoji da su saka dokar hana fita a birnin.

Tun a watan Disambar shekarar da ta gabata ne al'ummar kasar ta Indiya ke boren adawa da sabuwar dokar dan kasa, inda suke ta dauki-ba-dadi da jami'an tsaro. Musulmi da dama ne wannan rikicin ya tilsata musu barin gidajensu yayin da aka kona wasu masallatai a birnin na New Delhi.