Indiya: Korar madugun adawa daga majalisa | Labarai | DW | 25.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indiya: Korar madugun adawa daga majalisa

Madugun adawan kasar indiya Rahul Gandhi ya rasa kujerarsa ta majalisa bayan yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyu.

Madugun adawan Indiya Rahul Gandhin

Madugun adawan Indiya Rahul Gandhin

Ana dai zargin madugun adawan Rahul Gandhi da furta kalaman karya ga firaminista Narendra Modi bayan wani furici da ya yi kan wawure kudaden kasar.

Tun bayan da aka sanar da matakin na tube wa Rahul Gandhin rigarsa ta dan majalisa kafafen sadarwa a kasar ke bayyana damuwa kan makomar koma dimukuradiyyar kasar.

Ko da shi kansa madugun adawan Rahul Gandhi ya ce wannan wani mataki ne na yi masa bita da kulli da shi da masu adawa da gwamnatin Narendra Modi wace ta kuduri aniyar yin karan tsaye ga dumukudiyya.