1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 27 sun mutu a tashin gobara

Abdul-raheem Hassan
May 14, 2022

Jamai'an kashe gobara sun kwashe mutane kusan 50 a ginin da wutar ta tashi a wata cibiyar hada hada a birnin New Delhi, ana kuma neman sauran mutanen da suka makale a cikin benen.

https://p.dw.com/p/4BI8M
Indien Brände in den Vororten von Neu-Delhi
Hoto: Dinesh Joshi/AP Photo/picture alliance

hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 27 a tashin gobarar, wasu da dama sun jikkata bayan da wutar ta tashi a wani benen kasuwanci mai hawa hudu a New Delhi babban binrin kasar Indiya a ranar Juma'a, hukumomi sun ceto mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran Indiya Press Trust ya ce mutane 12 sun kone, an kuma kwashe wasu 50 daga benen bayan da jami'an kashe gobara suka shafe fiye da sa'o'i biyar suna kokarin shawo kan lamarin.

Yanzu haka dai ana ci gaba da neman sauran mutanen da suka makale a cikin ginin, sai dai kawo yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba. Firaiministan Indiya Narendra Modi ya bayyana kaduwarsa kan asarar rayuka daga gobarar. 

Irin wannan tashin gobarar dai ta zama ruwan dare a Indiya, inda ake zargin magina da saba dokokin gini da ka'idojin kariya.