1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Barazanar mummunar ambaliyar ruwa

July 26, 2023

An fara aikin kwashe mutane yayin da aka rufe makarantu a New Delhi na Indiya sakamamakon ambaliyar ruwa wanda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar.

https://p.dw.com/p/4UOkg
New Delhi, Indiya
Hoto: Adnan Abidi/REUTERS

Hasashen saukar ruwan sama mai karfi a yankin ya tilasta fara kwashe jama'a makwanni biyu bayan da kogin Yamuna ya tunbatsa kana ruwa ya mamaye bakin kogunan yankin, lamarin da ya haifar da kwashe daruruwan mutane. 

Daruruwan motoci ne dai suka nutse a garin Noida sakamakon cikar kogin. Ana dai hasashen samun saukar ruwan sama matsakaici a wannan Larabar a birnin na New Delhi. Hukumomi na cewa, ruwa ya fara kai wa kan bangon ginin tunawa da tsohon gwarzon kasar, Mahatma Gandhi