IMF ta ce tattalin arzikin Najeriya zai ja baya a 2016 | Siyasa | DW | 01.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

IMF ta ce tattalin arzikin Najeriya zai ja baya a 2016

Asusun Lamuni na Duniya IMF da Christine Lagarde ke shugabanta ya bayyana cewar bunkasar tattalin arzikin Najeriya zai ragu idan aka kwatanta da hasashen da aka yi tun da farko. Lamarin da zai zama koma baya a kasar.

Saurari sauti 03:34

Rahoto kan hasashen bunkasar tattalin arzikin Najeriya

Wani rahoton IMF ya ce karuwar tattalin arzikin kasar zata ragu daga kaso 3.2 da hukumar tai hasashe can baya ya zuwa kaso 2.3 sakamakon kara lalacewar lamura a bana.

Ko bayan rashin tabbaci na farashin man fetur din da ke neman mai da kasar 'yar rabbana ka wadatamu dai, ana kuma kallon wasu a cikin jerin manufofi na sabuwar gwamnatin da zama ummal aba'ísan lalacewar lamuran a fadar IMF din da ta ce ana bukatar sauyi a cikin gaggawa.

Rushewar harkoki na kasuwanci sakamakon rashin samun isassun kudaden ciniki na kasashen waje , game da raguwar farashin man fetur din da ya haifar da rage kudin batarwa a daukacin matakai na gwamnati da kuma damuwar tsaro ne dai suka hadu suka yi illa ga tattalin arzikin da a baya ke zaman mafi saurin girma a nahiyar Afirka gaba daya.

Sabon rahoton dai na nuna irin jan aikin da ke gaban mahukunta na kasar dake da alkawari na sauya rayuwa ta 'yan kasa amma kuma ke dada fuskantar matsalolin kudi da hali na rashin tabbas.

Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung

Faduwar farashin man fetur ta jawo wa Najeriya matsalolin kudi

Ko bayan rikin makamashi da mummunan karanci na wuta dai, tattalin arzikin kasar na kuma fuskantar jan gindi ga fara aiwatar da sabon kasafin kudin da yake fata zai zamo dan ba ta ragin radadin babun da ta mamaye ko ina cikin kasar.

A cewar Malam Yushau Aliyu da ke zaman masanin tattalin arzikin kasar, al'amuran sun yi tasiri wajen barazana ga tattalin arzikin kasar ta Najeriya .

Rashin tabbas kan kasafin kudin Najeriya

Tuni dai shugaban kasar ya ce zai yi karatun ta nitsu kafin rattaba hannu kan kasafin da wasu ke yi wa kallon dambar farfadowar lamura da ma kila tasiri wajen kai karshen matsalar da ta fyadi yara kuma ke hararar manyan cikin kasar ta Najeriya.

Abun kuma da ke iya kara daukar lokaci da ma kila sabon rikici a tsakanin bangaren zartarwar dake ganin da sauran sake , da kuma yan majalisar da dole ta tilsta wa kasafin da basu da wata sha'awa a ciki a karon farko cikin kusan 16 na dawowa bisa turbar demokaradiya a kasar.

Nigeria Symbolbild Korruption

Shugaba Buhari ya fara yaki haikan da cin hanci da rashawa

To sai dai kuma babbar matsala a tunanin Dr Kole Shettima da ke zaman shugaban cibiyar demokaradiya da ci gaban kasa da ke a Abuja na zaman rashin alkiblar tattalin arzikin da ya sa da kamar wuya 'yan jari na waje su yi gaggawar saka jarin da a ke bukata domin sake ginin ababe na more rayuwa.

A cikin makon da ya shude ne dai wani taro na masu ruwa da tsaki a kan tattalin arikizi ya yanke shawarar saka tsabar kudi har Naira Miliyan Dubu 350 da nufin agaza wa kamfanonin da su kai nisa wajen rage ma'aikata da ma barazana ta tsaida ayyuka gaba daya.

Sauti da bidiyo akan labarin