IITA: Shekaru 50 na tallafawa aikin noma a Najeriya | BATUTUWA | DW | 24.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

IITA: Shekaru 50 na tallafawa aikin noma a Najeriya

Cibiyar IITA da ke gudanar da bincike da kuma habaka aiyyukan noma ta cika shekaru 50 ta na gudanar da aikinta a tarayyar Najeriya. Cibiyar ta tallafa wajen ciyar da harkokin noma gaba a bangarori daban-daban a Najeriya.

Habaka aikin noma dai na daga cikin irin batutuwan da wannan cibiya ta IITA ta sanya a gaba daga kafuwarta a shekarar 1967 kawo wannan lokaci. Cibiyar dai na da masana kimiyya da ke gudanar da bincike kan abinda ya danganci inganta harkar noma musamman ma dai zamanantar da ita ta yadda manoma za su samu amfani mai yalwa kana a saukaka musu aikin nomansu.

Landwirtschaft Kenia Ernte von Grünen Bohnen (Getty Images/AFP/T. Karumba)

Samar da iri mai nagarta da zai samar da yabanya mai kyau na daga cikin aiyyukan da IITA ke yi

Shirye-shirye ne dai dama wannan cibiya ta IITA ke samarwa wanda suka hada da samar da iri mai nagarta da kuma shawarwari kan irin abinda ya kamata manomi ya shuka a gonarsa bisa la'akari da yanayin kasar da ya ke da ita. Baya ga wannan cibiyar na kuma samar da taki wanda ke taimakawa kasar noma ko da kuwa an fuskanci fari ko kanfar ruwan sama bayan manomi ya rigaya ya yi shukarsa.

Irin wadannan aiyyukan da IITA din ke yi ne ma ya sanya Kwamared Ya'u Musa Sakaba da ke jagorantar manoman rani a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ya ce irin hobbasa din cibiyar ta yi a shekarun suka gabata ba zai kimantu ba, don haka ya shawarci takwarorinsa manoma da su hada kai da IITA din don cin gajiyar irin aikin da suke yi.

Russland - Landwirtschaft - Traktor (picture-alliance/RIA Novosti/G. Kotov)

IITA ta lashi takobin yin aiki da matasa a jihohin Najeriya don habaka aikin gona a kasar

Albarkacin cikar wannan cibiya shekaru 50 da kafuwa, guda daga cikin manyan jami'an cibiyar Dr. Moses Ngala ya ce nan gaba  IITA din za ta girka ofisoshinta a dukannin jihohin Najeriya don bada gudummawa wajen habaka aikin gona musamman ma ga matasa. A cewarsa, cibiyar tasu za ta bada tallafi ga matasa dubu daya a kowacce jiha don basu dama ta samun kudin shiga da kuma wadata kasar da abinci.

Sauti da bidiyo akan labarin