ICC za ta wanke Uhuru Kenyatta? | Labarai | DW | 18.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC za ta wanke Uhuru Kenyatta?

An bukaci kotun hukunta lefukan yaki ta kasa da kasa ICC da ke a birnin Hague da ta wanke Uhuru Kenyatta

Lauyoyin zababben Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta za su nemi kotun duniya da ke hukunta masu manyan laifukan yaki(ICC), ta yi watsi da tuhumar da ake masa, bayan da aka sallami Francis Muthaura da ake musu tuhuma iri daya.Keyyatta yana fuskantar tuhuma bisa laifi akan bil Adama, bayan zaben shekara ta 2007 da aka samu tashin hankali.

Cikin wannan wata na Maris Keyatta ya lashe zaben shugaban kasar ta Kenya da aka gudanar cikin kwanciyar hankali da tsanaki, amma babban mai kalubalantarsa Firaminista Raila Odinga ya nufi kotu, saboda zargin tafka magudi.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas