Hukuncin kisa ga membobin Boko Haram a Chadi | Labarai | DW | 28.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin kisa ga membobin Boko Haram a Chadi

Kotun da ke sauraron manyan laifuka a kasar Chadi, ta yanke wa wasu mutane 10 da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne hukuncin kisa, bayan kamasu da laifi.

Wannan shari'a da ta gudana a wannan Jumma'a ta tabbar da hukuncin kisa ga duk mutanen goma, sannan kuma kotun ta ce makaman da aka kama za a mika su ga hannun gwamnatin kasar ta Chadi. Sannan wasu kayayyaki na razanar da al'umma, su kuma za a lalatasu. Wannan dai shi ne karo na farko da aka gudanar da wata shari'a kan wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a kasar ta Chadi. Mutanen goma dai, an kama su ne da laifin shirya kai hare-haren kunar bakin wake da suka yi sanadiyar rasuwar mutane da dama a watan Juni a birnin na Ndjamena fadar gwamnatin kasar.