Hukumomin kasar Masar sun zartar da hukuncin kisa ga mutane 15 | Labarai | DW | 26.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin kasar Masar sun zartar da hukuncin kisa ga mutane 15

A wasu gidajen yari biyu na kasar ta Masar aka rataye mutane 15 wadanda aka samu da laifin kai wa jami'an tsaro hari a yankin Sinai, inda 'yan tarzoma ke yawaita kai hari.

Ägypten Truppen im Nord-Sinai (picture alliance/AP Photo/Str)

Sojojin Masar dai na yawaita kai sintiri a arewacin yankin Sinai don dakile 'yan tarzoma

Hukumomin kasar Masar sun zartar da hukuncin kisa ga mutane 15 da aka samu da laifin kai hari ga jami'an tsaro a yankin Sinai kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta sanar a wannan Talata.

Mutanen dai an rataye su a cikin wasu gidajen yari guda biyu, inda ake tsare da masu laifin tun lokacin da kotun sojan kasar ta yanke musu hukunci sakamakon harin da suka kai Sinai inda 'yan ta'adda suke kai hari.

Wannan dai shi ne babban hukuncin kisan kai irinsa na farko a arewacin Afirka tun bayan rataye wasu mutane shida masu ikirarin Jihadi a shekara ta 2015 a kasar. Ratayar ta zo makwanni bayan kungiyar IS ta kaiwa wani jirgin yaki mai saukar angulu hari a filin saukar jiragen sama da ke arewacin yankin Sinai daidai lokacin da ministan harkokin cikin gida da na tsaro suke wata ziyarar aiki. Harin da ya yi sanadiyyar rasa ran mai tsaron lafiyar ministan tsaron kasar tare da matukin jirgin.

Kungiyar ta'adda ta IS tare da takwararta ta kasar Masar sun hallaka daruruwan jami'an tsaro a yankin na Sinai.

Kotunan kasar dai sun yanke wa mutane da yawa hukunci sakamakon tarzoma da tashe-tashen hankulan da karsar ta tsinci kanta a ciki tun daga lokacin da soja suka hambarar shugaba Mohammed Morsi a shekara ta 2013.

Shugaban kasar ya ba sojoji umarnin kawo karshen hare-hare a kasar cikin watanni uku.