Hukumar DSS ta kame wasu alkalai a Najeriya | Labarai | DW | 09.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar DSS ta kame wasu alkalai a Najeriya

Alkalai biyar ne jami'an tsaro da ke sanya fararen kaya wato DSS suka sanar da kamesu a sumamen da suka kai a gidajen wasu alkalai da ake zargi da cin hanci da karbar rashawa.

Supreme Court Abuja, Nigeria (DW)

A Najeriya hukumar leken asiri ta cikin gida wato DSS ta sanar da kame wasu alkalan kasar su kimanin biyar dama kudade da yawansu ya kai Dalar Amirka dubu 800 a lokacin wani sumame da jami'anta suka kai a gidajen alkalai daban-daban a duk fadin kasar a karkashin shirin nan na yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar ta kaddamar. 

A cikin wata sanarwa da ta fitar hukumar ta DSS ta ce sumamen wanda jami'anta suka gudanar bayen samun wasu bayanai na cin hanci da rashawa da saba ka'idojin aiki da ake zargin wasu alkalan kasar da aikatawa, kana sun kame wasu kadarori na miliyoyin Naira da tarin wasu takardu masu dauke da bayanai da ka iya kasancewa hujjoji na zargin da ake yi wa alkalan. 

Sai dai tuni kungiyar alkalai dama wasu kungiyoyin kare hakin dan Adam na kasar suka soki lamirin aikin kamen alkalan wanda suka ce yadda aka gudanar da shi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ta Najeriya.