1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Najeriya da watsi da 'yan cirani

August 27, 2019

Kungiyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakkin dan Adam a duniya ta ce mafi yawan mata da yaran da suka dawo gida bayan safararsu a kasashen waje na komawa sakamakon rashin kulawar hukumomi a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3OYxW
Nigeria Flüchtlinge kehren nach Lagos zurück
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/S. Alamba

Cikin wani rahoto mai taken "ka yi addu'a ka mutu", Human Right Watch din ta ce babu kulawa ta musamman game da lafiya da makor dubban mata da yaran da suka dawo daga aikin bauta sakamakon safararsu zuwa kasashe na waje. Rahoton mai shafi 90 ya tabo irin azabtarwar da daruruwan matan suka fuskanta a kan hanyar zuwa kasashen Turai da Gabas ta Tsakiya da ma yadda in sun dawo gida gwamnatin kasar kan yi burus da bukatunsu duk da nau'in cututukan da sukan dauko da ma tsananin fatara da talaucin da ta tilasa su aikin bautar. Agnes Odhiambo mai bincike ta musamman kan mata da kananan yara ta kungiyar  ta HRW ta ce ta yi hira da mata 76  da suka dawo daga kasashen duniya dabam-dabam da sunan safarar.

“Za ka dauka cewar bayan an ceto matan nan da yara wahala ta kare musu, amma abun ba haka yake ba. Matsalar na ci gaba bayan an dawo da su Najeriya. Ku tuna wadanan mutane ne da suka gudu daga iyalan da ke takura musu a wani lokaci ma su suke kai su gidan tsaffi bautar, a lokacin da suka dawo bayan share shekaru daya ko biyu ba tare da samun ko taro ba. Sannan kuma ga matsalar rashin lafiya ga ciwuka na zamani ga kuma tsanannin fatara, sai su tarar daukin da suke sa ran samu bai isa ba”

Nigeria Flüchtlinge kehren nach Lagos zurück
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/S. Alamba

Rahoton dai ya ce ana tilasta musu sana'o'in da ba su da sha'awa a wasu lokuttan ma ana garkame su a mutsugunan gyara hali ko sun so ko sun ki, a yayin kuma da ba sa samun wani daukin da zai taimake su fara sabuwar rayuwar da suke da bukata a fadar Abdulghaniyu Abubakar da ke zaman shugaban Kungiyar Save The Childe Innitiative da kuma ya taka rawa wajen binciken na wattani 18.

To sai dai kuma in har rashin kular tana zaman babban hatsari ga kasa, a tunanin mahukuntan matsalar 'yan koman da ma masu tunanin laifi a cikin dawowar na da ruwa da tsaki da batun al'ada maimakon halin ko-in-kula a fadar Hajara Yusuf da ke zaman wata mai gabatar da kara a ma'aikatar shari'ar Tarrayar Najeriyar da kuma ke cikin yakin safarar ta mutane.

Nigeria Flüchtlinge kehren nach Lagos zurück
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/S. Alamba

 Rahoton dai ya mai da hankali ne a biranen Legas da na Benin da Abuja, abun kuma da a cewar Human Right Watch din ke da ruwa da tsaki da yawan 'yan safarar. To sai dai kuma a fadar Sani dantumi Bello da ke shugabantar Freedom For Life Innitiative da ke yakin safarar matsalar na nan a arewacin kasar katutu.