1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

HRW ta zargi Kamaru da gaza dakile cin zarafin mata a kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 24, 2026

Kamaru ta ce mata 77 abokan zamansu maza suka kashe a shekarar 2024, wanda Human Rights Watch ta ce alkaluman sun haura.

https://p.dw.com/p/5FxZC
Shugaban Kamaru Paul Biya da mai dakinsa Chantal Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya da mai dakinsa Chantal BiyaHoto: Welba Yamo Pascal/AP Photo/picture alliance

Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta duniya Human Rights Watch, ta zargi gwamnatin Kamaru da gaza tabuka komai wajen yakar mummunar ta'adar nan ta cin zarafin mata a kasar, wanda ke ci gaba da karuwa a kullum.

Rahoton da Human Rights Watch ta fitar ranar Laraba, ya ce duk da alkawarin da mahukuntan Kamaru suka yi a shekarar 2011 na dakile wannan matsala, har yanzu abin kara habaka yake, musamman bangaren yadda mazaje ke gallazawa matansu na aure ko 'yan mata abokan zamansu.

Karin bayani: Kungiyar Human Right Watch ta koka da karuwar kame masu mu'amalar jinsi daya a Kamaru 

Wata kididdiga da hukumomin Kamaru suka fitar, ta nuna cewa mata 77 abokan zamansu suka kashe a shekarar 2024, wanda Human Rights Watch ta ce alkaluman sun haura haka, kasancewar ba dukkan mace-macen ake kai rahoton afkuwarsu ba.

Karin bayani:  

Rahoton hadin gwiwar tsaro tsakanin Kamaru da Najeriya

A shekarar 2023 ne hukumar bunkasa kasashe da tabbatar da daidaito ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP, ta sanya Kamaru a matakin kasa ta 148, daga cikin 162, wadanda ke gaza samar da daidaito a sha'anin bayar da ilimi da kiwon lafiya da kuma aiki a duniya.