Karuwar kamen masu mu'amalar jinsi dayaa Kamaru
April 15, 2021Talla
A cewar kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Right Watch daga watan Fabarairu zuwa yanzu an kama sama da mutum 24 a kasar. Lamarin da ta yi tir da shi.
Kungiyar ta ce ta sanar da hukumomin da ke da ruwa da tsaki a kan rahoton ta na yadda ake musgunawa wadannan mutanen da ke neman jinsi guda amma kama daga ma'aikatar shari'a da jami'an 'yan sanda babu wanda ya ce mata uffan a kan wannan lamarin.
Kamaru dai kamar sauran kasashe a nahiyar Afirka mu'amala ta masu neman jinsi daya na samun tirjiya daga al'umma da ma hukumomi, wanda idan aka gurfanar da mutum a gaban kuliya zai iya samun shekaru har biyar a gidan gyara hali.