HRW ta ce Boko Haram na cin zarafin al′uma | Siyasa | DW | 29.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HRW ta ce Boko Haram na cin zarafin al'uma

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta fitar da wani rahoto kan yadda kungiyar Boko Haram ta Najeriya ke shigar da kananan yara aiki soja da kuma yi wa mata fyade.

A cikin rahoton kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch, ta nuna karara yadda 'yan Boko Haram ke kama mata da yara mata da karfi, ciki akwai 'yan shekaru 12 da haihuwa. Sannan kungiyar ta kashe daruruwan mutane cikin hare-hare, kuma samar da kungiyar farar hula mai yaki da Boko Haram ya sauya fasalin rikicin.

Cikin hira da kungiyar Human Right Watch da mutanen da abin ya shafa, yayin ziyara a biranen Kano da Maiduguri kimanin mutane 60 sun bayyana irin hakuba a hannu Boko Haram. Mausi Shegun jami'ar hukumar a Tarayyar Najeriya, ta yi karin haske kan binciken:

"Maiduguri ne babban wurin da muka gudanar da bincike. Maiduguri yanzu da lokacin da muka gudanar da bincike akwai zaman lafiya, inda muka samu dama ta tambayoyi wa mutanen da muka saka a cikin rahoton. Haka yana da sauki saboda mutane suna shirya wajen bayyyana abin da ke faruwa."

Wata kungiyar farar hula da ke aiki da hukumomin tsaro ta samu nasarar kwato mata 26 da 'yan Boko Haram suka sace, yayin samame kan tungar kungiyar ta Boko Haram da ke dajin Sambisa. Wasu daga ciki suna da juna biyu sakamakon fyaden, wasu kuma sun haihu. Mafi yawan mata an kama lokacin da suke gona, wani lokaci a kan tituna musamman cikin kauyuka.

Wani lokaci 'yan Boko Haram kan shiga gida su bai wa iyaye kudi a matsayin sadaki, wani mutumi da bai amince ba, sai suka hallaka shi, sannan suka sace yarinyar. 'Yan Boko Haram sun kuma yi garkuwa da wasu mata lokacin da suka tare hanyar Benisheikh, da kusa da Damaturu da Gamboru. Amma ko rashin aiki na daga cikin dalilan da ya janyo 'yan Boko Haram ke shigar da yara kanana, jami'ar hukumar ta Human Right Watch a Najeriya, Mausi Shegun ta ce akwai wasu dalilan:

"Rashin aiki yana ciki, amma mafi yawan wadannan yara ya dace suna makaranta. Saboda haka rashin makarantu da rashinn kayan aiki, da rashin kudi daga bangaren iyaye, kuma babu hubbasan sauyawa daga bangaren gwamnati. Ga kuma talauci da ya yi katutu a kasar musamman yankin arewa maso gabashi da suka hada da jihohin Borno da Yobe."

A cikin wannan rahoto Human Right Watch ta ba da misali da wata yarinya 'yar shekaru 15 da haihuwa, wadda 'yan Boko Haram suka sace, ta dawo gida bayan watanni da tsohon ciki. 'Yan Boko Haram kuma suna kashe mutane musamman a kan hanyoyi da kauyuka. Gwamnatin Najeriya ta kafa dokar ta baci wadda yanzu aka tsawaita da karin watanni shida, domin dakile tashin hankalin da ake faruwa. Amma akwai sauran fata, har ila yau ga Mausi Shegun:

"Ina tsammanin matsayin kafar dokar ta baci shi ne tunkarar matsalolin tsaron daga bangarori daban-daban, ba wai dakile shigar da yara aikin soja ba kawai. A gaba daya tabbatar da zaman lafiya. Akwai zaman lafiya a Maiduguri lokacin da muke can, kuma wannan zaman lafiya na Maiduguri ya janyo kauyuka na cikin wahala."

Kungiyar ta Human Right Watch ta ce wasu lokuta dakarun kasar na wuce makadi darawa, yayin da suke bakin aiki. Sannan ta nemi gwamnati da dauki matakin hukuntan duk wanda aka samu da cin zarafin dan Adam.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin