Hong Kong: An yi barazanar fadada bore
September 30, 2014Talla
Sakataren kungiyar daliban Hong Kong din Alex Chow ya ce muddin jagoran Hong Kong din Leung Chun-ying ya gaza fita zuwa dandalin nan na Civic Square kafin tsakar daren yau, to kuwa karin dubban mutane na yankin za su bazama kan tituna don neman ganin an biya musu bukata.
Mr. Chow ya ce dalibai a halin yanzu na duba yiwuwar kara daukar mataki kan wannan fafutuka da ake yi inda ya kara da cewar in hakarsu ba ta kai ga cimma ruwa ba to za su tabbatar an yi yajin aikin gama-gari a Hog Kong din da kuma mamaye gine-gine gwamnati baki daya.