Hollande na ci gaba da ziyara a Afirka | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hollande na ci gaba da ziyara a Afirka

Shugaba François Hollande na Faransa ya kai ziyara a kasashen Angola da kuma Kamaru a wani rangadi na kwanaki uku da ya soma a kasashen uku na nahiyar Afirka.

Bayan da ya ziyarci kasar Benin a karon farko na wannan ziyarar, Shugaban na Faransa na tare ne da rakiyar manya-manyan shugabannin kanfanonin kasarsa akalla 50, abun da ya sa ake ganin wannan ziyara duk da cewa ziyara ce ta karfafa dangantaka, ziyara ce kuma ta harkokin kasuwanci tsakanin kasashen. Musamman ma kasar ta Angola mai arzikin man fetur da ke kuma da fada a ji a fuskar dipolomasiyar Afirka.

An dai rattaba hannu kan kwangiloli masu yawa a kasar ta Angola, tare da kanfanoni kamar su Total, Accor, Eiffage, Meteo France. Sannan kuma hukumar AFD "Agence Française de Développement" ta sanar da buda cibiyarta a birnin Luwanda na kasar ta Angola.

Hakan dai na nunin cewa an samu jittuwa tsakanin kasashen biyu inda shugaban na Faransa ya kiyaye tabo batun cin hanci da kare hakin dan Adam a kasar ta Angola. Da yammacin ranar Jumma'a ne dai shugaban na Faransa Francois Hollande ya sauka a birnin Yaounde na kasar Kamarun inda zai kammala wannnan ziyara.