1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shara a matsayin abin da ke kawo kudi

November 13, 2019

Wata matsashiya a Gombe na tattara shara tare da sarrafa ta zuwa wasu abubuwa domin samun kudi, inda kuma ta koyawa mata da 'yan mata har ma da samari wanann san'ar domin samun abin dogaro da kansu.

https://p.dw.com/p/3Svnj
Nigeria Umwelt Müll
Amfani da shara domin samar da makamashi da kayan kwalliyaHoto: DW

Matashiya Khadija Abubakar Bobbo wacce ta ke kokarin kamala digirin digirgir, ta na sarrafa kusan kowace irin shara zuwa abin da za a iya sayarwa ko kuma a yi amfani da shi a gida domin kawa ko sauran amfanin yau da kullum. Daga cikin abubuwan da take sarrafawa akwai bawon gyada da dusar shinkafa da bawon kwakwa, inda ta ke yin gawayi da ake girki da shi wanda baya hayaki kuma ya na biyan bukatar iyalai. Haka kuma Khadija na sarrafa takardu da kwalaye gami da robobin ruwa da aka watsar zuwa kayan kawata gidaje da ofisoshi da kuma sarrafa leda zuwa abin da ake gyara gidaje da su.

Khadija ta ce kwalliya na biya mata kudin sabulu da wannan sana'a kasancewar ta na samun nasarar tsabtace muhalli tare da farantawa al'umma musamman matan aure ta hanyar koya musu abin dogaro da kai. Sai dai babban Kalubalen da ta ke samu shi ne na karancin masu gidan rana da za ta rinka sayen kayayyakin aiki ta na koyawa matasa da kuma yadda matasan da dama ba sa ci gaba da sana'ar bayan sun koya. Masana na ganin wannan hobbasa ta matashiya Khadija da riba biyu, wato na samar da sana'a da kuma alkinta muhalli, musamman ganin yadda sauyi ko kuma dumamar yanayi ke addbar al'umma a duniya baki daya.