1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Minna HdM: Matashiya mais arrafa man gashi a birnin Minna

Uwais Abubakar Idris
February 19, 2020

A Najeriyas wata matashiya da ta yi karatun har matakin digiri na biyu a garin Minna da ke jihar Niger ta rungumi sana’ar sarrafa man gashi na mata, sana’ar da a yanzu take ba ta damar dogaro da kai.

https://p.dw.com/p/3Y0t4
Elfenbeinküste Frau bei Friseur in Abidjan
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

A Najeriyas wata matashiya da ta yi karatun har matakin digiri na biyu a garin Minna da ke jihar Niger ta rungumi sana’ar samar da man gashi na mata, sana’ar da a yanzu ta samar mata da dogarao da kanta da kuma yaye mata wata damuwa ta rashin gashi ga diyarta.

 
A Najeriya ba kasafai ake samun matan 'yan boko ba da suka yi karatu har matakin digiri, da amma kuma su ka rungumi kanana sanao’i maimakon jiran aikmin gwamnatin da a Zahiri a yanzu babu shi. Sai dai ga Fatimah Zara Usman lamarin ba haka yake ba, domin akwai abin da ya sanya ta zagewa ta rungumi sana’ar samar da mai irin dabam-dabam na gyara gashi musamman ga mata har ma da maza, domin har man da ake shafawa gemu da wanda ke kawar da sanko.

 
Ya zuwa yanzu dai Fatimah ta kai ga tsayawa da kafafunta a sana’ar da ta fara da Naira dubu uku, inda har kasashen Afrika ta Kudu, Amurka da Ingila ake sayen kayanta. Akwai dai ma’aikata mata da maza da suke aiki a karkashinta kuma ana biyansu albashi duk wata. Matasa da suka yi karatu a Najeriya kan ta gwagwarmayar samun aikin gwamnati ko na ofis, amma Fatimah ta ce ko da an ba ta zabi tsakanin aikin gwamnati da wannan sana'a tata, to ba shakka sana'ar sarrafan man gashin za ta zaba domin dogaro da kai ya fi, kana a cewarta aikin na ba ta lokacin gudanar da wasu abubuwan na daban.


Kokari na dogaro da kai muhimmi ne ga matasa a Najeriya musamman a dai dai lokacin da gwamnati ke cewa wadanda suka gama jami’a su nemi aikin yi don ba za ta iya wadata kowa da aiki ba.