Himma dai Matasa: Matashiya mai saka koma | Himma dai Matasa | DW | 09.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Himma dai Matasa: Matashiya mai saka koma

Wata matashiya mai suna Hadiza Auwal ta rugumi sana'ar saka abun kama kifi da ake fi sani da koma, wanda ba kasafai ake samun mata da yin wannan sana'ar ba.

Kolumbien Fischer auf Tierra Bomba in Bucht von Cartagena

Komar kama kifi

Bayan kammala karatunta na boko ne dai, matashiyar ta zabi ta yi wannan sana'ar da za ta dogara da ita wace a cewarta ba sai ta yi aikin gwamnati ba za ta samu dukkan rufin asirin da take bukata. Hadiza Auwal ta bayyana cewa ta samu nasarori a wannan sana'ar, koda yake akwai kalubalen da take fuskanta.

Burin matasa da dama dai, da zaran sun kammala karatunsu su samu aikin gwamnati, sai dai ra'ayin Hadiza ya sha bam-ban da na su. A bisa nasarorin da ta samu a wannan sana'ar, Hadiza ta yi kira ga 'yan uwanta matasa kan muhimancin sana'ar hannu. Masana na ganin, in har matasa za su tashi tsaye su rungumi sana'ar hannu, za'a samu raguwar rashin ayyukan yi da matasan ke fama da shi a Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin