Himma dai Matasa: Mai sana′ar kayan makulashe | Himma dai Matasa | DW | 06.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Himma dai Matasa: Mai sana'ar kayan makulashe

Wata matashiya a jihar Sakkwato da ke Najeriya, ta rungumi sana'ar yin kayan kwalam da makulashe domin rufa wa kanta asiri.

Rukayya Abubakar Bajah matashiya ce da ke ajin karshe a jami'a, amma kuma ta rungumi sana'ar kayan makulashe, inda take yin gullisuwa da kwakumeti da carbin malam da makamantansu. Matashiyar dai ta rungumi sana'ar ne a wani mataki na  kaucewa rashin aikin yi da kuma dogaro da kai.

A cewar matashiya Rukayya Bajah ta samu alkhairi mai yawa sakamakon sana'ar tata, kuma tana daukewa kanta kudin makaranta da  sauran lalurorin yau da kullum, baya ga matasa da take koyawa sana'ar da kuma wadanda ke taimaka mata suke kuma cin abinci a karkashinta.

Sauti da bidiyo akan labarin