SiyasaGabas ta Tsakiya
Rikicin Isra'ila da Hezbollah ya dagule
June 3, 2026
Talla
Kungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta yi barazanar kai hare-hare biranen Tel Aviv da Haifa na Isra'ila, domin mayar da martani kan hare-haren Isra'ila a kudancin birnin Beirut fadar gwamnatin kasar Lebanon.
Yanayin da ake ciki
Wannan gargadin na zuwa lokacin da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila yake cewa dakarunsa za su kai hare-haren birnin Beirut, muddun kungiyar Hezbollah mai alaka da Iran, ba ta daina kai hare-haren kan Isra'ila ba.
Wani hari na jirage maras amatuka na Isra'ila ya halaka mutane shida a kudancin Lebanon da kuma kudancin birnin Beirut. Lamura suna kara dagulewa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah duk da shiga tsakanin da Amurka ta yi.