1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya samar da manhaja a Gombe

August 4, 2021

Abu-Ubaida Muhammad wani matashin ne dan jarida a Gombe da ke Tarayyar Najeriya, da yake da bai war kirkirar Manhajar sada zumunta.

https://p.dw.com/p/3yXm9
Symbolbild I BigTech I Social Media
Matashi ya kirkiri manhajar da ka iya yin aiki tamkar sauran kafofin sada zumuntaHoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Manhajar sada zumuntar ta Abu-Ubaida Muhammad dai, za a iya amfani da ita a wayoyin sadawar kamar yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na zamani na WhatsApp da Facebook da makamantansu.

Matashi Abu- Ubaida ya sanyawa manhajar tasa da ya kirkira suna "Daychat." A cewarsa ya samu nasarori masu tarin yawa sakamakon wannan manhaja da ya kirkira, koda yake ba a rasa kalubale.