1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: Matashi mai kera na'urorin jirgi

October 14, 2020

A daidai lokacin da rashin ayyukan yi ke jefa wasu matasa cikin kungiyoyin masu gwagwarmaya da makamai, wani matashi mai suna Abubakar Abba ya fara kirkirar wasu na'urori da jirage ke amfani da su.

https://p.dw.com/p/3jvsH
Screenshot | HdM: Maiduguri Flugzeug Ersatzteile
Matashin da ya kera jirgin sama mai saukar ungulu a Najeriya

Matashin Injinaya Abubakar Dalori ya kasance mai kokarin kirkirar abubuwa da ake wahalar samu, abin da ya kai shi ga fara kirkirar wasu na'urorin jirgin sama mai saukar ungulu. Da wannan kokari nasa ne ma har ya kera jirgi mai saukar ungulun, a dakin kere-kerensa. Sai dai saboda dalilai na tsaro ba a bar shi ya tayar da jigin kamar yadda ya so ba. Banda na'urorin jirgin sama da Injiniya Dalori ke kerawa, yana kuma yin wasu na'urori na amfanin gida da wuraren aiki, wanda suke saukakewa al'umma harkokin rayuwa.

Ganin akwai bukatar rungumar matasa domin su samu ayyukan yi, ya sa Injiniya Dalori ya koyar da matasan, kuma da yawancinsu sun samu hanyar dogaro da kansu. Ya ce koyar da matasan, na daga cikin nasarorin da ya ke ya samu a rayuwarsa. Sai dai duk wannan nasarori da ya cimma a rayuwarsa, Injiniya Dalori ya ce ya na fama da matsaloli. Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum dai, na ganin akwai bukatar gwamnatoci a dukkanin matakai, su taimakawa wannan matashin, saboda bunkasa tunaninsa domin kara kwarin gwiwa ga matasa. Matashin dai ya ce ba zai iya jinginme sana'arsa ya kama aikin gwamnati ba, in akwai wani abu na gwamnati da ya ke neman bai wuce tallafi ba.