Sakkwato: Matashi mai sana'ar gadaje
August 4, 2020Shi dai wannan matashi Mustapha Ibrahim Magaji Gusau ya ce tun yana jami'ar jihar Sakkwato inda ya yi karatunsa kafin ma a kai ga batun karewa, ya soma sana'ar yin gadaje da kujerun na alfarma da kuma fannin dirowowi da ake sakawa a kicin, inda ya ce ya kwashe kusan tsawon shekaru biyu yana wannan sana'ar.
To sai dai kuma matashin ya ce sana'ar tattare take da tarin kalubale, wanda kullum burinsa yaga ya magance su. Koda yake duk da irin kalubalen da matashin ke fuskanta, ya ce akwai tarin nasarorin da ya samu a sana'ar. Burin Mustapha wanda yanzu haka matasa da dama ne dai ke koyon aikin kafintan a wurinsa domin samun kudin hidimar yau da kullum, shi ne fatan samar da wani katafaren kamfanin kera gadaje da kujerun alfarma da zai samar da gurabun ayukkan yi ga dimbin matasan jihar ta Sakkwato.