HdM: Mai lalurar kafa na tuka Keke-Napep | Himma dai Matasa | DW | 13.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

HdM: Mai lalurar kafa na tuka Keke-Napep

Wani matashi mai fama da lalura ta rashin kafafu, ya rungumi sana'ar tuka Keke-Napep domin samun abun da zai dogara da kansa.

Matashin mai suna Mustapha Isma'il ya shahara tsakanin 'yan uwansa matasa a jihar Adamawan. Wannan matashi mai lalura ta musamman da ke tafiya da gwiwowinsa, ya ce ya rungumi sana'ar ne maimakon ya rinka yin bara ko maula kamar yadda wasu masu lalura irin tasa ke yi.

Matashin ya kara da cewa bayan ya kammala karatunsa na boko ne, ya ga bai kamata ya jira aikin gwamnati ba abin da ya sanya shi rugumar wannan sana'ar domin ya dogara da ita, ya kuma samu nasarori da dama a wannan sana'ar, koda yake akwai kalubalen da ba za a rasa ba.

Masana na ganin da gwamnati za ta tashi tasye wajen karfafa wa matasa gwiwa domin su rugumi sana'ar hannu kamar yadda Mustapha ya yi, da za a samu raguwar rashin ayyukan yi da ma rayuwar zauna gari banza da ke zama barazana ga harkokin tsaro a Najeriyar.
 

Sauti da bidiyo akan labarin