1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin mota ya kashe mutane a Kenya

October 10, 2018

Sama da mutum 40 ne suka mutu sakamakon wani hadarin motar safa kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/36GG7
Kuba Busunglück
Hoto: picture alliance/dpa/O.-A. Sosa

Alkaluman mahukunta na cewa akalla mutum 42 ne suka mutu a hadarin da motar kira bas ta yi a yankin yammacin kasar.

'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar samun karuwar wadanda za a rasa, saboda munin hadarin wanda ya kai ga kwaye rumfar motar.

Motar dai na kan hanyarta ne ta zuwa Kakamega daga Nairobi, tana kuma dauke ne da fasinjoji 52.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce motar ta tintsire ne, kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga tabbatar da musabbabin hadarin ba.

Kimanin mutum dubu 12 ne ke mutuwa a duk shekara a Kenyar, sakamakon hadarin ababen hawa.