Hatsarin jirgin ruwa a China | Labarai | DW | 07.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsarin jirgin ruwa a China

Akalla mutane 32 suka bace bayan da wasu jiragen ruwa guda biyu suka yi karo da juna a tekun China kana kuma daya ya kama da wuta.

Jiragen ruwan wanda daya na dakon fasinja ne da kuma mai dakon man fetir sun yi taho mu gama a tsakiyyar ruwan tekun na China kuma take jirgin dakon man fetir din ya kama da wuta. Ministan sufiri na China ya ce 30 daga cikin mutanen da suka mutu 'yan kasar Iran ne da kuma biyu 'yan Bangladesh.